A yayin wannan zabe, za a zabi sabbin 'yan majalisar wakilai masu aikin kafa dokokin kasar su 435, tare da 'yan majalisar dattawan kasar 35, da wasu gwamnonin jihohi, da manyan kwamishinonin dake kula da yankunan kasar Amurka dake ketare, da wasu magajin muhimman biranen kasar.
Zaben da ya fi jan hankalin mutane shi ne zaben wasu sabbin 'yan majalisun dokokin kasar biyu, wato muhimmin fage da jam'iyyar Democrat, da ta Republican suke fafatawa da juna.
Yanzu haka dai mambobin jam'iyyar Republican, su ne ke da rinjaye a wadannan majalissu biyu. (Sanusi Chen)