in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da hukumar kula da harkokin yawan shakatawa ta XE
2018-04-10 10:29:34 cri
A jiya Litinin aka kafa hukumar kula da harkokin yawon shakawa ta yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin domin samarwa kananan kamfanonin yankin damammakin ciniki.

Kimanin kananan kamfanonin yankin 6 ne aka dunkulesu karkashin hukumar ta Xinjiang Equity Exchange wato (XEE) a takaice.

Mataimakin manajan hukumar ta XEE, Ma Qing, ya bayyana cewa, hukumar zata taimaka wajen tallafawa kananan kamfanonin yankin tafiyar da harkokin kudadensu, da kuma tattara muhimman bayanan kamfanonin, kana zai taimakawa gwamnati wajen shiryawa da kuma aiwatar da tsare tsarenta.

An kafa hukumar ne bisa hadin gwiwar XEE da kungiyar yawon bude ido ta yankin Xinjiang.

Samar da tsarin daidaito na shiyya yana daga cikin muhimman manufofin kasuwar hada hadar kudade ta kasar Sin, wanda galibi take samar da ayyukan hidima ga kamfanonin da ba na gwamnati ba, domin basu dama ta bai daya a bangaren tafiyar da harkokin kudade.

A shekarar data gabata, yankin Xinjiang ya karbi bakuncin masu yawan bude ido sama da miliyan 100, wanda shine adadi mafi yawa a tarihi. Bangaren ya lashe kudi da yawansu ya kai yuan biliyan 180 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 28.5, wato an samu karin kashi 30 bisa 100 ke nan. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China