A cewar ratoton da hukumomin gudanarwar yankin suka fitar, yankin ya samar da sabbin guraben aikin yi ga mutane dubu 470, kuma an dauki hayar mutane kimanin miliyan 2.75 daga yankunan karkara. Sama da gidaje dubu 368 dake kananan garuruwa aka yiwa kwaskwarima, kana magidanta dubu 300 dake yankunan karkara ne aka samar musu sabbin gidajen zama.
Gwamnatin yankin ta bayyana shirinta game da rage radadin talauci ne a farkon wannan wata.
A kokarin gwamnatin kasar Sin na kawar da matsanancin talauci, da kuma kafa wata al'umma mai matsakaiciyar wadata nan da shekarar 2020, gwamnatin yankin Xinjiang ta himmatu wajen inganta wasu yankuna 22 mafiya fama da talauci, kuma gwamnatin za ta tsame dukkan mazauna yankunan dake rayuwa cikin kangin talauci. (Ahmad Fagam)