Hukumar ta bayyana a yau Alhamis cewa, masu yawon bude idon sun kuma kashe Yuan biliyan 2 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 314 a lokacin bikin na tsawon mako guda wanda ya kare a jiya Laraba, karuwar sama da kaso 28 cikin 100 kan na shekarar bara. Kuma yankunan karkara da wuraren wasanni na lokacin sanyi na daga cikin wuraren da maso yawon bude idon suka fi son ziyarta. (Ibrahim Yaya)