in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jaddada bukatar daukar matakan yaki da ta'addanci a yankin Xinjiang, in ji wani jami'i
2018-02-12 13:42:34 cri

Babban jami'in JKS mai kula da yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashinsa na kasar Sin Chen Quanguo ya bayyana cewa, akwai bukatar kara mayar da hankali kan daukar matakan yaki da masu kokarin kawo baraka gami da ayyukan ta'addanci a yankin, a wani mataki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Chen ya yi wannan kira ne yayin zantawarsa da jaridar Peoples Daily ta JKS, yana mai cewa, sama da masu yawon bude miliyan 100 daga cikin gida da wajen kasarsa ne suka ziyarci yankin a shekarar da ta gabata, lamarin dake nuna cewa, akwai cikakken zaman lafiya da tsaro a yankin.

Ya ce, abin da shugabannin yankin suka sanya a gaba shi ne, samar da cikakken zaman kafiya da tsaron jama'a. A don haka wajibi ne a yi la'akari da batun zaman lafiya yayin da ake kokarin gudanar da ko wane irin aikin a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China