in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya mikawa sabuwar tawagar kashe gobara da ceton al'umma tuta
2018-11-09 20:04:40 cri

A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya mikawa sabuwar tawagar kashe gobara da ceton al'umma ta kasa sabuwar tuta, inda ya umarce su da su kasance masu biyayya ga jam'iyya, da nuna da'a da sadaukar da kai ga jama'a.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban askarawar kasar, ya jaddada cewa, kamata ya yi tawagar ta zauna cikin shiri a duk lokacin da jama'a ke bukatarsu, su kuma yi kokarin ceto rayukansu daga bala'u, tare da taimaka musu a lokacin da suka shiga wata matsala gami da ceton rayuka da ma dukiyoyinsu.

An dai kafa tawagar kashe gobara da ceton al'umma ce bisa ayyukan kashe gobara na kasar da 'yan sandan kula da gandun daji.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China