in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya gana da Henry Kissinger
2018-11-08 20:48:33 cri
A yau Alhamis ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Henry Kissinger a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana Kissinger a matsayin tsohon abokin Sinawa. Yana mai cewa ba zai taba mantawa da irin gudummawar tarihi da ya bayar ba wadda ta kai ga alakar kasashen Sin da Amurka.

Xi ya kara da cewa, duk da irin kwan gaba kwan baya da ake fuskanta, alakar kasashen biyu na tafiya yadda ya kamata cikin shekaru arba'in da suka gabata.

Ya ce yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba cikin shekaru 100 da suka gabata, har yanzu al'ummar duniya na fatan cewa, alakar Sin da Amurka za ta ci gaba da wanzuwa bisa tafarkin da ya dace.

Shugaban na Sin ya kuma bayyana cewa, shi da shugaba Trump na Amurka sun amince su gana yayin taron kolin G20 da za a yi a kasar Argentina, inda bangarorin biyu za su yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan dake janyo hankalinsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China