"Abin farin ciki ne matuka kuma abinda ba za'a taba mantawa ba ganawata da shugaba Xi Jinping," Diaz-Canel ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Shugaban kasar na Cuban ya gana da shugaba Xi ne a ranar Alhamis din data gabata a birnin Beijing, inda dukkannin bangarorin biyu suka jaddada aniyarsu ta mutunta al'adunsu na abokantaka da kuma kafa sabon babi game da alakar dake tsakanin kasashen biyu.
"A matsayin wata al'ada da hangen makoma a nan gaba, kasar Sin ta bude kofarta a yayin da wasu ke kokarin gina katangar rufe kofarsu," inji shugaban na Cuban a sakonsa na Twitter.
Diaz-Canel ya fada a cikin karin wani sakon sa cewa, "bisa ga irin cigaban fasaha da kasar Sin ta samu da kuma kara bude kofarta ga kasashen duniya," hakan ya samarwa duniya kwarin gwiwa na samun kyakkyawar makoma a nan gaba.
Diaz-Canel, wanda ya isa birnin Shanghai a ranar Talata domin fara ziyarar aikin kwanaki 3 a kasar ta Sin, yace kasar Cuba tana matukar yabawa irin goyon bayan da kasar Sin take bata marar iyaka, da kuma cigaba da nuna goyon bayan da take baiwa sabbin shugabannin Cuba bisa dadaddiyar al'adar abokantaka dake tsakanin kasar Cuba da kasar Sin.