in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin zai halarci taron rikon kwarya karo na 26 na kungiyar APEC
2018-11-12 11:36:57 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya sanar da cewa, bisa gayyatar da babban kwamishina Bob Dadae, da firamista Peter Oneil na kasar Papua New Guinea da kuma sarki Haji Hassanal Bolkiah na Brunei, and shugaba Rodrigo Duterte na jamhuriyar Philippines suka yi masa, shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai ziyara wadannan kasashe uku, tsakanin ranakun 15 da 21 ga watan Nuwamban da muke ciki, kuma zai gana da shugabannin kasashe tsibiran dake tekun Pacific wadanda suka kulla dangantakar diflomasiyya da kasar Sin a Papua New Guinea. Bugu da kari, bisa gayyatar da firamista Peter Oneil na kasar Papua New Guineada ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron rikon kwarya karo na 26 na APEC da za a yi a garin Port Moresby na kasar Papua New Guinea a tsakanin ranakun 17 da 18 ga wannan watan. (Sanusi Chen)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China