in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka tana goyon bayan kafa yankin tsaro a Syria, in ji ministan wajen Rasha
2017-05-07 12:55:12 cri
Kwanan baya, aka cimma wani mihimmin sakamako a yayin taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria karo na hudu da aka yi a birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda aka kulla yarjejeniyar kafa yankunan tsaro guda hudu a duk fadin kasar Syria.

Haka kuma, a ranar 6 ga wata, aka gabatar da cikakken bayani kan batun gina yankunan tsaro hudu a kasar Syria ta shafin intanet na ma'akatar harkokin wajen kasar Rasha. Kuma an cimma ra'ayi daya kan wannan bayanin da aka fito a yayin taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria da aka yi a birnin Astana a ranar 3 da ranar 4 ga watan nan da muke ciki, kana, za a fara yin amfani da bayanin tun daga ranar 6 ga wata.

Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Amurka ta aike da sabbin ma'aikata masu sa ido da su halarci sabon taron shawarwarin, inda suka yi hadin gwiwa da kasashen Rasha, Iran, Turkiya da kuma Syria da dai sauran kasashen da abin ya shafa wajen warware matsalar kasar Syria ta hanyar siyasa.

Bugu da kari, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, kasar Amurka ita ma tana goyon bayan kafa yankunan tsaro a kasar Syriar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China