in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karfin musayar cinikin dake tsakanin Sin da kasashen "Ziri daya da hanya daya" ya wuce RMB biliyan 6000 cikin farkon watanni 9 na bana
2018-10-26 11:06:49 cri
Bisa labarin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta fidda a jiya Alhamis, an ce, cikin farkon watanni 9 na shekarar bana, karfin musayar cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake cikin shirin "Ziri daya da hanya daya" ya wuce RMB biliyan dubu 6, adadin da ya karu da 13% idan aka kwatanta da na makamancin lokaci a bara.

A fannin gine-gine kuma, ana tafiyar da harkokin layin dogo na Addis Ababa-Djbouti, tashar jirgin ruwa ta Piraeus da kuma layin dogon Mombasa-Nairobi cikin yanayi mai kyau. Kuma ya zuwa yanzu, kamfanonin kasar Sin sun kafa yankunan hadin gwiwar cinikayya guda 82 a kasashen, inda suka samar da haraji ga kasashen na kimanin dallar Amurka miliyan 2010, tare da samar da guraben aikin yi kimanin dubu 244 a wadannan kasashe. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China