Shawarar, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013, ta hada da shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar Siliki ta ruwa na karni na 21. Manufarta ita ce, habaka cinikayya da gina kayakin more rayuwa a hanyar da ta hada nahiyar Asiya da Turai da kuma Afrika, a an tsohuwar hanyar siliki.
Hassan Al-Saouri, shehun malami a sashen kimiyyar siyasa na Jami'ar Al Neelain ta Sudan, ya ce tun da farko Sudan ta amince da shawarar ta kasar Sin, kuma ta bayyana shirinta na zama babbar abokiyar hulda.
Shehun malamin ya ce a matsayin Sudan ta mahadar kasashen Afrika da na Larabawa, za ta iya taka muhimmiyar rawa a cikin shawarar.
Shi ma Abdul-Rahim Al-Sunni, mai sharhi kan al'amuran siyasa a cibiyar binciken harkokin siyasa da tattalin arziki ta Khartoum, ya ce kasarsa za ta fi amfana da ayyukan makamashi dake cikin shawara. (Fa'iza Mustapha)