Hua ta jaddada cewa, a cikin abokan hadin gwiwa na Sin, babu wata kasa da ta fuskanci rikicin basussuka sakamakon hadin gwiwa tare da kasar Sin. Rikicin basussukan da ya faru da ake magana a kai ba shi da nasaba da kasar Sin.
Hua Chunying ta bayyana cewa, wasu kasashe masu tasowa suna fuskantar matsin lamba kan tattalin arzikinsu, kana an samu juyin juya hali da fuskantar bala'u a wasu kasashe, wasu matsaloli da aka fuskanta na dan wani lokaci a aikin "ziri daya da hanya daya" matsala ce da aka saba fuskanta yayin da ake kokarin samun bunkasuwa, kuma tilas a warware su ta hanyar yin shawarwari a tsakanin bangarorin da abin ya shafa. Sin tana fatan kafofin watsa labaru za su rika bayar da labaran gaskiya cikin adalci bisa hakikanin halin da ake ciki daga dukkan fannoni. (Zainab Zhang)