in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa za su yi hadin gwiwa a fannin makamashi
2018-10-19 11:25:13 cri

Kasar Sin da kasashe 10 da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa sun yi alkawarin zurfafa hadin gwiwa wajen samar da makamashi domin samun sabbin cigaban fannin makamashi a kasashen.

Kasashen sun yi wannan alkawari ne a cikin sanarwar hadin kai da suka bayar a yayin taron ministocin makamashi bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", wanda aka gudanar a birnin Suzhou dake gabashin kasar Sin.

Hadin gwiwar makamashin ta kasance wata muhimmin fanni a karkashin shawarar ta ziri daya da hanya daya. Tun bayan kaddamar da shawarar shekaru 5 da suka gabata, an riga an gudanar da jerin muhimman ayyukan makamashi cikin nasara, wadanda suka haifar da gagarumin cigaban yanayin zamantakewa da tattalin arzikin kasashen.

Mahalarta taron sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su kara kaimi wajen yin hadin gwiwa a fannin samar da makamashi, da warware matsalolin da suka shafi cigaban makamashi mai tsabta, da hanzarta sauya nau'in makamashi a duniya, da kuma yin hadin gwiwa wajen bunkasa samar da ingantaccen makamashi mai tsabta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China