in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu bunkasar cinikayya da zuba jari tare da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya
2018-08-28 09:52:11 cri
Cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta samu bunkasa a fannin cinikayya da hada hadar zuba jari, tare da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya.

Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron ganawa da manema labarai, mataimakin minista a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Qian Keming, ya ce darajar hada hadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen dake cikin shawarar ta kai sama da dalar Amurka tiriliyan 5, yayin da matsakaicin karuwar da hakan ke yi ya kai kaso 1.1 bisa dari, duk da koma baya da ake samu a harkokin cinikayyar duniya.

Mr. Qian Keming, ya kara da cewa, Sin ta zamo abokiyar huldar cinikayya mafi girma ga kasashe 25 dake cikin wannan rukuni. Ya ce karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen da ke bin shawarar ziri daya da hanya daya, an samar da yankunan raya tattalin arziki da bunkasa cinikayya 82, wadanda jimillar jarin dake tsakanin su ya kai dalar Amurka biliyan 28.9.

Har ila yau, wadannan yankuna sun jawo sassan masu zuba jari har 4,000, tare da samar da kudaden haraji da suka kai dala biliyan 2 ga kasashen, baya ga guraben ayyukan yi 244,000 da suka samarwa al'ummun yankunan su.

Kasar Sin dai ta sanya hannu kan gina, ko daga matsayin yankunan ciniki cikin 'yanci 5 tsakanin ta da kasashe 13 da suka amince da shawarar.

Shawarar ziri daya da hanya daya da aka gabatar a shekarar 2013, ta kunshi manufar hade yankunan nahiyoyin Asiya, da Turai, da Afirka da hada hadar cinikayya, da kuma samar da ababen more rayuwar jama'a.

A nasa tsokaci, mataimakin shugaban ofishin raya shawarar ziri daya da hanya daya Ning Jizhe, ya ce Sin ta sanya hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa 118 tare da kasashe da yankuna da kuma hukumomin kasa da kasa 103, da nufin raya shawarar ta ziri daya da hanya daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China