Shugaba Xi Jinping ya gabatar da sakon ne a Juma'ar nan ta kafar bidiyo. Ya ce wannan shawara ta samu matukar karbuwa tsakanin kasashe masu tarin yawa.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, kasashen da suka amince su shiga a dama da su a cikin shawarar, suna ci gaba da tuntubar juna a wajen tsara manufofi, da gaggauta aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi raya tattalin arziki da cinikayya. Har ila yau suna mai da hankali matuka wajen hade sassan manyan ababen more rayuwa, da bunkasa hadin gwiwa a bangaren raya masana'antu da hada hadar kudade, da karfafa musaya tsakanin al'umma, matakan dake haifar da tarin alfanu ga jama'ar kasashen.