in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar ziri daya da hanya daya ta kasance kashin bayan ci gaban harkokin cinikayyar lardunan kasar Sin
2018-08-07 13:59:33 cri
Bayanai na nuna cewa, shawarar ziri daya da hanya ta sanya yankunan kasar Sin da ba su wajen mashigin teku kasancewa a kan gaba cikin manufar bude kofa ta kasar, inda aka samu bunkasar harkokin cinikayya tsakanin yankunan dake yammaci da tsakiyar kasar da ma kasashen dake cikin wannan shawara.

Galibin yankunan sun samu ci gaban harkokin cinikayya a watanni shida na farko na wannan shekara karkashin wannan shawara, idan aka kwatanta da ci gaban su a harkokin cinikayya baki daya.

Lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin ya samu karuwar kaso 53.9 cikin 100 a harkokin cinikayya tsakaninsa da kasashen dake cikin shawarar, idan aka kwatanta da kaso 31.7 cikin 100 da ya samu a baki dayan harkokin cinikayyarsa.

Shi ma lardin Gansu dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin ya samu irin wannan ci gaban harkokin cinikyayya da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, inda ya karu da kaso 41 cikin 100, karuwa kadan kan bunkasuwar harkokin cinikayyar lardin baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China