in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Falesdinu ya gana da mataimakin shugaban Sin
2018-10-24 16:18:59 cri
Bisa gayyatar da gwamnatin Falesdinu ta yi masa, mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya kai ziyarar aiki a kasar a jiya Talata, inda ya gana da firaministan kasar Rami Hamdallah a birnin Ramallah.

A yayin ganawar tasu, Wang Qishan ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan za a warware sabanin dake tsakanin Falesdinu da Isra'ila ta hanyar yin shawarwari cikin lumana, kuma bisa tushen "daftari na kasashe guda biyu". Kuma kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa wajen sabunta tsarin yin shawarwarin dake tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za a warware matsalar Falesdinu cikin yanayin adalci kuma bisa dukkan fannoni.

Haka kuma, ya ce, kasar Sin tana maraba kwarai dangane da shigar Falesdinu cikin shirin "Ziri daya da hanya daya", kuma za ta sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Falesdinu, domin ba da taimako ga bunkasuwar kasar.

A nasa bangare kuma, Rami Hamdallah ya ce, kasarsa tana yabawa matuka da goyon bayan da kasar Sin ke baiwa al'ummomin kasar, da kuma matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun Falesdinu. Ya ce kasarsa tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a fannonin gina ababen more rayuwa da ciniki da dai sauransu, a yayin da take dukufa wajen gina shirin "Ziri daya da hanya daya" da kasar ta Sin, ta yadda za a inganta huldar zumuncin dake tsakanin Falesdinu da Sin yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China