in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Isra'ila sun harba boma-bomai zuwa wurin sintiti dake arewacin yankin Gaza
2018-05-29 14:03:40 cri
Jiya Litinin, sojojin Isra'ila suka fidda sanarwa cewa, sun harba boma-bomai wani wurin sintiti dake arewacin yankin Gaza, kuma rahotannin da Falesdinu ta fitar na nuna cewa, harin ya haddasa rasuwar mutum daya, yayin da wani kuma ya jikkata.

Haka kuma, sojojin Isra'ila sun ce, a wannan rana, sun gano Falesdinawa guda biyu a kan yankin dake tsakanin arewacin Gaza da Isra'ila, a kokarinsu na shiga cikin Isra'ila daga yankin Gaza. Sun kuma kara da cewa, a yayin da suke bin wadannan mutane biyu, wasu Palasdinawa suka rika harbinsu da bindigogi daga yankin Gaza, sa'an nan, sojojin Isra'ila sun mayar da martani ta hanyar harba boma-bomai zuwa wani wurin da Falesdinawa ke sintiri.

Jami'an tsaron yankin Gaza sun bayyana cewa, a wannan rana, sojojin Isra'ila sun harba boma-bomai zuwa wani wurin sintiti na kungiyar Hamas ta Falesdinu dake arewacin yankin Gaza. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China