in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu ya karu
2018-10-14 16:53:30 cri
Kwanan baya, rikicin dake tsakanin Isra'ila da Falesdinu ya karu cikin sauri, lamarin da ya haddasa jikkata da rasuwar mutane da dama. Wasu na ganin cewa, al'ummomin Falesdinu sun rasa sukuni wajen samun zaman lafiya sabo da goyon bayan da kasar Amurka take nunawa Isra'ila, sa'an nan, sun sake daukar makamai domin maida martani kan Isra'ila. Lamarin da ya kara haifar da tarnaki wajen neman sulhu a tsakanin bangarorin biyu, yayin rikice-rikice a tsakaninsu ke ci gaba da wanzuwa.

A ranar 12 ga wata, wata 'yar Falasdinu ta rasu sakamakon harin da Yahudawa suka kai mata a yammacin kogin Jordan. A wannan rana kuma, rikici ya kaure a tsakanin wasu Falesdinawa da sojojin Isra'ila a zirin Gaza, wanda ya haddasa rasuwar Falesdinawa guda 7, yayin da guda 252 suka jikkata.

A ranar 7 ga wata, wani dan Falesdinu ya kai hari ga 'yan Isra'ila a yammacin kogin Jordan, lamarin da ya haddasa rasuwar 'yan Isra'ila guda biyu, yayin da guda daya ya jikkata. Sa'an nan, a ranar 11 ga wata, wani dan Falesdinu ya yiwa wani sojan tsaron kasar Isra'ila rauni da wuka a wani wurin dake kusa da birnin Nablus, yayin da wata mace ta ji rauni bisa kuskure a yayin rikicin.

A watan Afrilu na shekarar 2014, an dakatar da shawarwarin neman sulhu a tsakanin Falesdinu da Isra'ila. Sa'an nan, a ranar 6 ga watan Disamba na shekarar 2017, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da mayar da birnin Jerusalem fadar mulkin Isra'ila. A ranar 14 ga watan Mayu kuma, kasar Amurka ta kaurar da ofishin jakadancinta daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Jerusalem. Falesdinu ta nuna damuwa matuka kan wannan batu, kuma ta ki yarda ta dawo teburin shawarwarin neman sulhu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China