Yajin aikin ya kunshi na hada hadar kasuwanci, da bankuna, makarantu, jami'o'i da hukumomin gwamnati a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.
A kalla Palastinawa 15 ne aka hallaka, kana sama da 1,200 kuma suka jikkata a ranar Jumma'a a lokacin da dakarun Isra'ila suka bude wuta kan dandanzon Palastinawa wadanda ke gangamin ranar tunawa da kasarsu wanda suka gudanar a kan iyakar Gaza da Isra'ila.
Shugaban Palastinu Mahmud Abbas ya dora alhakin faruwar lamarin kan Isra'ila, kana ya ayyana ranar Asabar a matsayin ranar makoki ta kasa baki daya.
A wata sanarwar da ofishin firaministan Palastinu Rami Hamdallah ya fitar, ya bukaci kasa da kasa da su kawo karshen takaddamar dake tsakanin bangarorin biyu, yayin da babban batun dake zama jigo shi ne matsalar 'yan gudun hijira, bisa ga yarjejeniyar MDD mai lamba 194 da kuma batun kafa kasar Palastinu mai hedkwata a gabashin birnin Kudus. (Ahmad Fagam)