A wannan rana kuma, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh, ya gabatar da jawabi a wani masallaci dake birnin Gaza cewa, ba za a tsayar da zanga-zangar ba, har sai Isra'ila ta dena mamayar da ta yiwa yankin Gaza. Kana, ya kuma yi kira da a fadada wuraren gudanar da zanga-zangar zuwa yankin yammacin kogin Jordan.
Koda yake, wannan rana ita ce ranar Jumma'a ta farko bayan da aka shiga watan Azumi, 'yan Falesdinu da dama sun fita yin zanga-zangar a yankin dake kan iyakar tsakanin Falesdinu da Isra'ila a zirin Gaza. (Maryam)