in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya sake jaddada ra'ayin Sin na gaggauta warware batun Falesdinu ta hanyar siyasa
2018-04-27 14:48:45 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya yi hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa, wajen gaggauta warware batun Falestinu ta hanyar siyasa, kasancewar hakan zai dace da moriyar Falesdinawa, wanda shi ne kuma babban fatan al'ummomin yankin Gabas ta Tsakiya, har ma da dukkanin al'ummomin kasashen duniya.

A yayin taron muhawara kan batun Gabas ta Tsakiya da kwamitin sulhu na MDD ya kira a wannan rana, Ma Zhaoxu ya ce, kasar Sin tana goyon bayan ciyar da harkokin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya gaba, kuma tana goyon bayan yunkurin Falesdinawa na gina kasarsu mai 'yancin kai, wanda za a mai da gabashin birnin Kudus fadar mulkin ta, da kuma tsara yankin iyakarta bisa wanda aka shata tun a shekarar 1967. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China