A yayin taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD game da halin da ake ciki a Gaza, Yu Jianhua ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta goyi bayan yin amfani da makaman da ba su dace ba, kuma ta bukaci bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da aikace-aikacensu na tada hankulan al'umma. Kana, ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya tsai da domin gaggauta dawowar Isra'ila da Falesdinu teburin yin shawarwarin neman sulhu, ta yadda za a warware batun birnin Kudus ta hanyar zaman lafiya da yin shawarwari.
Haka kuma, ya ce, kasar Sin ta fidda manufofi guda hudu domin warware matsalar Falesdinu, kuma tana son yin shawarwari da gamayyar kasa da kasa kan batun Falesdinu a koda yaushe, ta yadda za a warware matsalar bisa dukkan fannoni, kuma cikin yanayin adalci. (Maryam)