Bisa labarin da aka samu, an ce, 'yan sandan kasar Morocco sun kama wadannan baki ne a lokacin da suke kokarin keta shingen da aka dasa a yankin iyakar dake tsakanin kasar Morocco da birnin Melilla na kasar Spaniya a ranar 21 ga wata. Kana, a wannan rana, mutane sama da dari 3 sun shirya keta yankin iyakar dake tsakanin birnin Melilla da kasar Morocco, wasu daga cikinsu sun cimma nasarar shiga birnin, yayin da 'yan sandan kasar Morocco suka kama mutane 141 daga cikinsu.
Bugu da kari, an ce, wani bako ya rasu sakamakon faduwar da ya yi daga kan shingen, yayin da baki 22 suka jikkata a lokacin da suka keta shingen, inda aka kai su asibiti. Ban da haka kuma, sojojin kasar Morocco sama da goma sun ji rauni a yayin da suka dukufa wajen hana wadannan baki keta shingen. (Maryam)