in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta amince da taron Bamako game da haramta shigo da kayayyaki masu illa cikin Afirka
2018-07-27 11:11:01 cri
A jiya ne mahukuntan kasar Morocco suka amince da sakamakon taron Bamako game da haramta shigo da kayayyaki masu hadari cikin Afirka da kula da zirga-zirgar a kan iyakokin kasashen da ma yadda ake sarrafa shara masu hadari a kasashen Afirka.

Manufar taron wanda kasashen na Afirka suka kirkiro a shekarar 1991 kana ya fara aiki a shekarar 1998, ita ce kare lafiyar al'umma da yanayin muhalli na kasashen Afirka, ta hanyar haramta shigo da duk wasu kayayyakin shara da dagwalon masana'antu ko na'urori masu hadarin gaske ga lafiyar bil-Adama. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China