Ministan ma'aikatar bunkasa birane, samar da gidaje da tsara ci gaban birane na kasar Morocco Abdelahad Fassi Fihri, da ministan kyautata muhalli da samar da ci gaba mai dorewa na kasar Benin Jose Tonato ne suka sanya hannu kan takardun yarjejeniyar.
Da yake tsokaci game da hakan, yayin bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Rabat, fadar mulkin kasar Morocco, Mr. Fassi Fihri, ya jaddada muhimmancin wannan yarjejeniya, yana mai cewa za ta baiwa kasashen biyu damar amfana da kwarewar juna, a fannin warware matsalolin bunkasa ci gaban birane.
A nasa bangare kuwa, Mr. Tonato cewa ya yi, kasar sa na fatan amfana daga kwarewar Morocco a fannin tsara manufofin kyautata yankunan ta. (Saminu Hassan)