A karon farko dokar ta tanaji haramci ga yiwa mata auren dole, da kuma cin zarafin mata ta hanyar talala da su.
Cikin watannin baya bayan nan dai, laifuka masu nasaba da cin zarafin mata a kasar na kara yawaita, matakin da ya sanya matan kasar gudanar da zanga zanga, domin matsawa gwamnati lambar samar da tsauraran dokoki, na hukunta masu aikata wannan ta'asa, ta kuma baiwa matan Morocco damar samun walwala a tsakanin al'umma. (Fa'iza Mustapha)