Sanawar da hukumar ta fitar, ta ce an fara shirye-shiryen kaddamar da layin dogon mai sauri da ya hada birnin Tangier, dake gabar teku da Casablanca, cibiyar harkokin kasuwanci ta kasar tun a watan Yuni.
Hukumar ta ce a ranar Litini za a kaddamar da gasar tsara tambarin jirgin ga duk wanda ke son bada gudunmuwa ga aikin da kasar ta yi domin al'ummarta.
Sabon jirgin dake gudun da ya zarce kilomita 352 cikin kowacce sa'a, zai rage tsawo lokacin da ake dauka yayin tafiya tsakanin Tangier da Casablanca daga sa'o'i 5 zuwa kimanin 2.
An shafe shekaru 10 ana aikin da ya lakume dala biliyan 2, wanda aka samu daga Moroocon da Faransa da Saudiyya da Kuwait da Hadaddiyar Daular Laraba. (Fa'iza Mustapha)