in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Morocco ya kulla yarjejeniya da kamfanin kasar Sin don yin ayyuka a Afrika
2018-09-18 10:28:31 cri
Bankin Attijariwafa (AWB), daya daga cikin manyan bankunan kasar Morocco, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da wani kamfanin gine-gine na kasar Sin (CSCEC) domin kaddamar da wasu manyan ayyukan hadin gwiwa a Afrika.

A wata sanarwar da bankin ya fitar a jiya Litinin ya ce, yarjejeniyar za ta baiwa bankin na AWB dama wajen gudanar da ayyukan hadin gwiwa na dogon lokaci tare da kamfanin na CSCEC, wanda ya kasance a matsayin babban kamfanin gine-gine a duniya, wanda ke gudanar da ayyukan gina kayayyakin more rayuwa da gidaje.

Bangarorin biyu zasu ci gajiyar damammakin harkokin cinikayya daga dukkan fannoni, wanda ya kunshin gina kayayyakin more rayuwa, da aikin gina rukunin gidaje a kasar Morocco da sauran kasashen Afrika inda bankin na AWB ke da rassa.

"Kasashen Afrika suna bukatar irin wadannan damammaki domin samun bunkasuwa", in ji shugaban bankin AWB, Mohamed El Kettani.

Ya kara da cewa, kwararrun jami'an kamfanin CSCEC da na bankin AWB da kamfanonin kasar Sin dake ayyuka a Afrika za su yi hadin gwiwa domin samar da kyakkyawan sakamako a nahiyar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China