in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron matan Afrika a Morocco
2018-09-28 11:53:39 cri
A jiya Alhamis aka bude taron kolin "mata a Afrika" wato (WIA) a takaice, a birnin Marrakech, na kasar Morocco, taken taron shi ne "nazari kan Afrika tare da nuna kwarin gwiwa da yin amana da kwarewar da nahiyar ke da ita".

Taron kolin ya samu halartar kusan mutane 400 daga kasashen duniya 70, da kasashe 50 daga Afrika da masu gabatar da jawabai daga kasa da kasa.

Sarkin Morocco Mohammed VI ya ce, matan Afrika sun cimma nasarori masu yawa a fagen ilmi da kuma kara shiga a dama da su a harkokin cinikayya, wanda hakan ya haifar da samun karuwar mata da suka shiga harkokin siyasa, tattalin arziki da sauran fannonin zamantakewar rayuwar al'umma.

A matsayin wani bangare na ci gaba, an bukaci Afrika da ta yi amfani da dukkan albarkatun da Allah ya huwace mata, musamman kwararrun matan da Afrikan ke da su, in ji sarki Muhammad.

Sarkin ya jaddada cewa, akwai bukatar a dauki karin matakai da za su kara baiwa mata damammakin yin gogayya da takwarorinsu domin samun dauwamamman ci gaba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China