in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da firaministar Burtaniya
2018-10-20 16:31:09 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana a jiya Juma'a, da Firaministar Burtaniya, Theresa Mary May a birnin Brussels, fadar mulkin kasar Belgium, a lokacin da suke halartar taron shugabannin kasashen Asiya da na Turai.

A yayin ganawar tasu, Li Keqiang ya bayyana cewa, an yi ganawar firaministocin Sin da Burtaniya a farkon shekarar nan, domin inganta hulda da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, inda suka cimma ra'ayi daya kan gaggauta aikin musayar dake tsakanin kasuwannin cinikin takardun hada-hadar kudi na birnin Shanghai da na birnin London, lamarin da ya sa, Burtaniya ta kasance kasa ta farko da ta fara musayar kasuwannin cinikin takardun hada-hadar kudi da kasar Sin. Ya ce a nan gaba kuma, kasar Sin tana son ci gaba da karfafa fahimtar juna dake tsakaninta da Burtaniya, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A nata bangare, Theresa Mary May ta ce, kasar Sin ita ce muhimmiyar abokiyar cinikayyar Burtaniya, kuma tana sa ran ziyarar firaminista Li Keqiang a kasarta domin gudanar da sabon zagaye na ganawar firaministocin kasashen biyu. Haka kuma, Burtaniya tana maraba da kara bude kofa ga waje da kasar Sin za ta yi, domin tana son ci gaba da raya huldar ciniki dake tsakanin kasashen biyu bisa tsarin shawarwari kan harkokin tattalin arziki da na kudi. .

Shi ma Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci ganawar tasu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China