in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Burtaniya ta yi dan karamin garambawul a majalisar zartarwar kasar
2018-07-10 10:02:27 cri
Rahotanni daga Burtaniya na cewa, firaminista Theresa May ta Burtaniyar ta yi wani dan kwarya-kwaryar garambawul a majalisar zartaswar kasar, inda ta nada sakatarori hudu biyo bayan ajiye aiki da tsohon sakataren harkokin wajen kasar Boris Johnson ya yi.

A daren jiya ne uwargida May ta nada sakataren lafiya Jeremy Hunt a matsayin sabon sakataren harkokin wajen kasar, don maye gurbin Johnson. Yayin da sakataren al'adu Matt Hancock ya maye gurbin Hunt, kana babban mai shigar da kara Jeremy Wright kuma ya maye gurbin sakatare Hancock a matsayin karamin sakataren harkokin sadarwa na zamani, al'adu, kafofin watsa labarai da wasanni. Sai kuma Geoffrey Cox wanda aka nada a matsayin atoni janar a majalisar zartarwar kasar.

Da farko dai ministan kula da ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai David Davis ne ya yi murabus daga mukaminsa, kana bayan wasu 'yan sa'o'i sai daya daga manyan ministocinta Johnson shi ma ya aje nasa mukamin.

Rahotanni na cewa, kusoshin gwamnatin nata sun yi murabus ne, kan shiryen-shiryen da Madam May ta gabatar game da ficewar Burtaniya daga EU, wanda suka ce ba su cika alkawuran da aka yiwa jama'a game da kuri'ar jin jama'a da aka kada a shekarar 2016 ba, inda galibin 'yan kasar suka nemi ballewa daga kungiyar EU. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China