in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gurfanar da masu kisan 'yan kasar Sin gaban kuliya, in ji shugaban Afirka ta Tsakiya
2018-10-20 16:28:27 cri
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera, ya ce tabbas za a gurfanar da wadanda ake zargi da laifin kisan 'yan kasar Sin a gaban kuliya, yana mai cewa babu wanda zai iya hana kasashen biyu karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Shugaba Touadera ya bayyana haka ne a birnin Bangui, lokacin da yake ganawa da jakadan Sin dake kasar.

Shugaba Touadera ya kuma sake jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, ya kuma yi Allah wadai da kakkausar harshe kan wadanda suka aikata laifin, ya na mai kiransu da masu adawa da raya kasar Afirka ta Tsakiya cikin zaman lafiya.

Ya kara da cewa, rikice-rikicen da ake yi a kasar cikin 'yan shekarun baya bayan nan, sun jefa al'ummomin kasar cikin damuwa, inda suke fatan za a kawo karshensu tare da neman ci gaba kasar cikin zaman lafiya. A don haka, ya kamata a ci gaba da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta Tsakiya, ba tare da la'akari da matsalolin da ake fuskanta ba.

A ranar 4 ga wata ne, wasu tsageru suka kai hari kan wasu Sinawa dake aiki a birnin Sosso-Nakombo dake kudu maso yammacin kasar Afirka ta Tsakiya, lamarin da ya haddasa mutuwar 3 daga cikinsu, yayin da wasu 3 kuma suka jikkata.

Rahotanni na cewa, 'yan sandan kasar sun riga sun cafke mutane fiye da goma dake da hannu cikin harin, sa'an nan, an fara gudanar da binciken shari'a a lamarin, a kuma watan Nuwamba mai zuwa ne za a fara sauraron karar a fili. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China