in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ya yi kira da a kara samarwa CAR tallafi
2017-11-10 12:42:31 cri

Jami'ar MDD dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Najat Rochdi ta yi kira da a kara taimaka wa kasar da yaki ya daidaita.

Najat ta kuma shaida wa manema labarai cewa, hukumomin agaji dake kasar ba su da karfin samarwa al'ummomin dake tsananin bukata wani karin taimako fiye da muhimman kayayyakin rayuwa. Ta ce, baya ga matsalar abinci, kasar tana fama da karancin magunguna da cibiyoyin kula da lafiya. A don haka bai kamata duniya ta juya mata baya ba.

Najat Rochdi ta kuma yi gargadin cewa, zai yi wahala galibi musulmi da kiristoci mabiya darikar Katolika da dama da suka rasa gidajensu su sassanta a tsakaninsu, baya ga sake wuraren Ibada da gidajen da aka lalata a fadan da ya barke tsakanin sassan biyu.

Tun a watan Mayun wannan shekara ce, al'amuran tsaro suka ci gaba da lalacewa a kasar, al'amarin da ya rikide zuwa mummunan tashin hankalin kabilanci da ba a taba ganin irinsa ba tun a shekarar 2014.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China