Antonio Guterres wanda ya kammala ziyarar kwanaki 4 da ya kai kasar ta Afirka ta Tsakiya, ya bayyana haka ne a jiya, a zauren majalisar dokokin kasar dake birnin Banji.
Sakatare Janar din ya kara da cewa, zai gabatar da shawarar kara yawan membobin tawagar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar ga kwamitin sulhu na Majalisar, don kara mata karfin sojoji.
Baya ga haka, Guterres ya bayyanawa membobin majalisar dokokin cewa, za a taimakawa kasar wajen kafa wata rundunar soji mai karfi sannu a hankali, wadda za ta maye gurbin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake kasar.
A halin yanzu, yawan membobin tawagar kiyaye zaman lafiyar ya zarce dubu 12 da dari 5, inda Guterres ya bayyana cewa, ya kamata a kara yawansu da 900. (Zainab)