in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici ya hallaka mutane 22 a kasar Afirka ta Tsakiya
2017-07-01 13:31:22 cri
Rahoto daga kasar Afirka ta Tsakiya na cewa, rikicin da ya barke kwanan baya a birnin Zemio dake kudu maso gabashin kasar, ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 22.

Rahoton ya ce, a ranar 28 ga watan Yuni ne, mazauna wata unguwa dake birnin Zemio da wasu 'yan banga suka yi taho-mu-gama, sakamakon wani rikicin kudi.

Bangarorin biyu dai, ba su gamsu da hukuncin kotu ba, abun da ya sa rikicin ya ta'azzara zuwa fada.

Sannan 'Yan banga daga birnin Bangassou dake gabashin kasar su ma sun shiga cikin fadan.

A halin yanzu, tawagar wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta girke a Afirka ta Tskiya ta kara tura wasu sojoji yankin don kwantar da tarzoma.

Rahoton ya kara da cewa, a ranar ta 28 ga watan Yuni, mutane 22 ne suka mutu sakamakon tarzomar. Amma saboda katsewar hanyoyin sadarwa, ba'a samu ainihin adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni ba a baya bayan nan.

Tun daga watan Maris din bana, yanayin tsaron da ake ciki a wasu sassan Afirka ta Tskiya ya dada tabarbarewa sakamakon wasu tashe-tashen hankula da suka barke.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China