in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da hari kan jami'an wanzar da zaman lafiya a Afirka ta Tsakiya
2017-07-25 13:49:11 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi kakkausan suka game da harin da aka kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, lamarin da ya haddasa rasuwar jami'in tawagar dan kasar Morocco daya, tare da jikkatar wasu jami'an 3.

Cikin wata sanarwa da mambobin kwamitin su 15 suka fitar, sun soki harin na safiyar jiya Litinin, suna mai cewa hakan na iya zama laifin yaki bisa dokokin kasa da kasa.

Kwamitin na tsaro ya kuma bukaci mahukuntan jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da su gaggauta gudanar da bincike, tare da tabbatar da gurfanar da masu hannu cikin sa gaban shari'a. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China