in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za mu iya koyon fasahohin Sin wajen kawar da talauci, in ji ministan tattalin arzikin Afirka ta Tsakiya
2018-05-23 12:50:26 cri
Kwanan baya, ministan kula da harkokin tattalin arziki, shiri da hadin gwiwar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Felix Moloua ya bayyana cewa, adadin masu fama da talauci na kasarsa ba ya raguwa, kuma kasar za ta iya koyon fasahohin kasar Sin, sa'an nan, ta yi kira ga al'ummomin kasar da su hada kai wajen kawar da talauci a kasar.

Bisa kididdigar da MDD ta yi, an ce, a halin yanzu, kimanin mutane miliyan 2.5 suna bukatar taimakon jin kai, adadin da ya wuce rabin yawan al'ummar kasa. Ya kuma kara da cewa, dandalin tattaunawar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka da za a yi, ya kasance kyakkyawar dama ga kasarsa wajen koyon fasahohin Sin na kawar da talauci.

Haka zalika, Mr. Moloua ya ce, ban da musayar ra'ayoyi da bangaren kasar Sin, tura jami'ai zuwa kasar Sin ita ma ta kasance dabara mai kyau ta koyon fasahohin kasar Sin. Sabo da ba kawai za su iya koyon fasahohin kasa kai tsaye ba ne, har ma za a iya kara fahimta kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a tallafawa al'ummomin kasar.

Bugu da kari, ya ce, shirin "Ziri daya da hanya daya" muhimmiyar dama ce da ya kamata a kama, kana, ya kamata a sake binciken shirin raya kasa, domin cimma nasarar shirin yadda ya kamata, ta yadda al'ummomin kasashen biyu za su ci gajiyar shirin tare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China