A shekarun baya baya nan, an sha samun tashe-tashen hankula a Afirka ta Tsakiya, gami da rikice-rikice a tsakanin kungiyoyin dakarun kasar, wadanda suka haddasa fararen hula da dama rasa gidajensu, an kuma kai wasu hare-hare kan masu aikin ceto da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya a kasar.
Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Stephen O'Brien ya bayyana bayan da ya kai ziyara Afirka ta Tsakiyar a watan Yuli cewa, rikicin dake faruwa tsakanin kungiyoyin dakarun kasar ya rikide zuwa kisan kare dangi. Alkaluman MDD na nuna cewa, a watan Yuli kadai, mutane kimanin miliyan 2 da dubu 400 ne ke neman agaji a kasar, adadin da ya kai rabin adadin al'ummar kasar. (Zainab Zhang)