in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin kudin da Sin ta zuba a aikin nazari ya wuce yuan biliyan 1760 a shekarar 2017
2018-10-10 15:40:14 cri
Jiya Talata, hukumar kididdigar Sin, da ma'aikatar harkokin kimiyya da fasaha, da ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin, sun fidda rahoto na "Adadin kudaden da Sin ta zuba a harkokin kimiyya da fasaha a shekarar 2017". Cikin rahoton, an ce, a shekarar 2017, adadin kudin da Sin ta zuba a aikin raya harkokin nazari da gwaje-gwaje watau R&D, ya wuce RMB yuan biliyan 1760, adadin da ya karu da kashi 12.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2016.

Haka kuma, bambancin dake tsakanin Sin da Amurka a fannin zuba kudade a aikin R&D yana raguwa bi da bi. A shekarar 2013, karo na farko kasar Sin ta hau matsayi na biyu a wannan fanni, kuma adadin kudin da Sin ta zuba a lokacin ya kai kashi 40 bisa dari na kudin da Amurka ta kashe, kana, bisa hasashen da aka yi, an ce, adadi na shekarar 2017 zai kai kashi 60 bisa dari idan an kwatanta da na kasar Amurka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China