Da take jawabi a wajen bikin bude taron mutum-mutumin inji na duniya na shekarar 2016, (WRC2016), wanda za'a gudanar har zuwa ranar 25 ga wannan wata, Madam Liu ta ce, bunkasa fasahar kera mutum-mutumin inji yana taimakawa matuka wajen samarwa masana'antu karin kwarewa, kuma ya taimaka wajen inganta kayayyakin da ake samarwa da cigaban rayuwar jama'a.
Liu tace "gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana matukar martaba rawar da kere kere ke takawa wajen samar da fasahar kera mutum-mutumin inji da cigaban masana'antu. Ana bukatar yin aiki tare da sauran kasashen duniya game da masana'antu masu basira, ciki har da masu kera mutum-mutumin inji, da kuma gina tsari mai cike da basira domin amfanar da rayuwar bil adama".
Taken taron shi ne "yin aiki tare domin cin moriya don gina al'umma mai cike da basira". Taron na bana ya samu halartar kamfanonin kera mutum-mutumin inji kusan 150 daga kasashe dabam dabam.(Ahmad Fagam)