Dan majalissar zartaswar kasar Sin Wang Yong, ya yi kira da a kara azama wajen gudanar da hadin gwiwa mai ma'ana, domin tabbatar da kariya ga ikon mallakar fasaha tsakanin kasashen dake cikin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, domin tabbatar da samun ci gaba a fannin kirkire kirkire.
Wang Yong wanda ya bayyana hakan jiya Talata, cikin jawabin taya murnar bude taron koli game da ba da kariya ga ikon mallakar fasaha na bana, na kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, a madadin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasashe da suka shiga wannan shawara, na bukatar karfafa dokoki da tsare tsaren, na kare ikon mallakar fasaha, su kuma yi hadin gwiwa wajen gudanar da al'amura a bayyane, cikin adalci da kyautata yanayin gudanarwa, ta yadda hakan zai kara inganta sashen ba da kariyar fasaha.(Saminu)