Wannan na kunshe ne cikin wani daftari da aka gabatar yayin taron kasa da kasa kan kera mutum-mutumi da kwaikwayon tunanin dan Adam, wanda aka kaddamar jiya Alhamis a yankin Wujiang na birnin Suzhou dake lardin Jiangsu na gabashin kasar Sin.
A cewar daftarin, darajar kayakin da masana'antun suka samar ta zarce yuan biliyan 70 a shekarar 2017. Kuma ana sa ran adadin zai karu zuwa sama da yuan biliyan 160 ya zuwa shekarar 2020. Inda ya kara da cewa, sana'ar za ta gaggauta habaka a nan gaba idan ta samu karin jari.
Kididdiga ta nuna cewa, an zubawa sana'ar jarin yuan biliyan 58.2 a bara, adadin da ya karu da kaso 60 akan na 2018.
Har ila yau, daftarin ya ce ana bukatar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam sosai a kasar Sin, inda ya bada shawarar kwalejoji da jami'o'i su kara kaimi wajen bada horo a bangaren. (Fa'iza Mustapha)