in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shirya manyan taruka biyu kan sabbin fasahohi a lokacin guda
2018-09-20 14:28:26 cri

Ta yaya dan-Adam zai ci gajiyar sabbin fasahohi? An amsa wannan tambaya a yayin manyan tarukan kasa da kasa guda biyu da aka shirya a lokacin guda a nan kasar Sin.

Daga ranar 17 zuwa 19 ga wata, an shirya babban taron fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam na kasa da kasa karo na farko a birnin Shanghai na kasar Sin, wanda ake kira "Gagarumin taron wasannin Olympics na fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam".

A sakonsa na murnar bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa na fatan hada kai tare da sauran kasashe a wannan fannin domin samun ci gaba tare, kiyaye tsaro tare, da kuma more nasarori. Wannan ya nuna cewa, kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da kara inganta dunkulewar duniya bai daya sun kasance muhimmin abubuwan da za su sanya sabbin fasahohi su kara samar da gajiya ga dan Adam.

Yanzu, daukacin al'umma na cikin lokaci na yin kwaskwarima kan masana'antu karo na hudu, wadda ke mai da hankali kan wasu sabbin fasahohi, ciki har da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, makamashi maras gurbata muhalli, fasahar mutum-mutumin inji, fasahar kwaikwayon hakikanan abubuwa da kuma fasahar halittu da dai sauransu.

A lokaci guda kuma, an kira wani babban taron kasa da kasa na daban, wato dandalin tattaunawar DAVOS na shekarar 2018, inda aka mayar da hankali ga batun kwaskwarimar masana'antu karo na hudu, da tattauna yadda za a kafa al'umma mai yin kirkire-kirkire. A yayin da yake halartar taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana manufofi guda uku game da kara karfin ci gaban tattalin arzikin duniya a yayin sabuwar kwaskwarimar masana'antu, ciki har da nacewa kan dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, da neman ci gaba da zai kunshi kowa da kowa, da inganta yin kirkire-kirkire da samun ci gaba yadda ya kamata, haka kuma an nuna cewa, ra'ayin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama shi ne zai taimakawa wajen ganin dan-Adam ya ci gajiyar sabbin fasahohi. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China