Antonio Guterrres, ya ce sauye-sauyen da yaduwa da saurin fasahohin zamani suka samar, abu ne da ba a taba gani ba, amma kuma matakin hadin gwiwar kasa da kasa ba kai wanda zai iya fuskantar kalubalen ba.
Ya ce a wannan lokaci na zamani, ana samun bayanai da fasahohi sosai, wanda ke bada dama ga kasuwanci da ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar wadanda ke da dama da ilimin amfani da su. A don haka, hadin giwar duniya abu ne mai muhimmanci wajen tabbatar da kowa ya amfana da wadannan fasahohin zamani.
A cewar Melinda Gates, idan dukkan mutane, musammam marasa karfi da masu rauni, za su samu damar amfani da fasahohin kamar sauran mutane, to za su yi amfani da shi wajen inganta rayuwarsu da na iyalansa, tare da bayyana ra'ayoyinsu game da makomar duniya. Ta na mai cewa tabbatar da wannan, shi ne aikin shirin.
Antonio Guterres, ya bukaci shirin ya bada gudunmuwa ga muhawarar al'umma ga muhimmancin hadin kai da amfani da dabarun daban-daban, domin tabbatar da an samar da makomar fasahar zamani mai aminci ga kowa, bisa kiyaye hakkokin bil adama. (Fa'iza Msutapha)