Ofishin kula da kare hakkin mallakar fasaha na kasar Sin ya ce kasar ta lashi takobin kafa karin cibiyoyin kare hakkin mallakar fasaha.
Shugaban Ofishin Shen Changyu, wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai na ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar, ya ce ya zuwa yanzu, an kafa irin wadancan cibiyoyin guda 19 a fadin kasar.
Manufar cibiyoyin ita ce, samar da managartan hanyoyin kare hakkokin mallakar fasaha cikin sauki da gaggauta tabbatar da hakkokin ga masu bukata.
A cewar jami'in, Kasar Sin za ta karfafa kare hakkin mallakar fasaha domin sauke nauyin dake wuyanta, tare kuma da kara takarar tattalin arzikinta.
Kasar Sin ta karbi bukatar samun hakkin mallakar fasaha miliyan 1.38 kan wasu kirkire kirkire a shekarar 2017, adadin da ya karu da kaso 14.2, wanda kuma shi ne adadi mafi yawa da aka taba samu cikin shekaru 7. (Fa'iza Mustapha)