Kwamitin raya ciniki tsakanin kasa da kasa na kasar Sin, da kwamitin harkokin masana'antu da kasuwanci na kasar Sin dake B20, sun fidda wata sanarwa a madadin kungiyoyin masana'antu da na kasuwanci, suna masu cewa, sun halarci wannan taro cikin himma da kwazo, inda suka ba da shawarwari masu amfani da dama, kan batutuwan da aka tattauna a yayin taron. Sun kuma bayyana ra'ayoyin kasar Sin kan kyamar kariyar ciniki, da inganta kwaskwarima ga kungiyar WTO yadda ya kamata, da dai sauransu. Haka kuma, sau da dama, sun tattauna da mashirya taron, inda suka gabatar da shawarwarinsu kan yadda za a gyara takardar.
Amma cikin sanarwar da suka fitar, an ce, taron B20 ta musanta bukatun da kungiyoyin masana'antu, da na kasuwanci na kasar Sin suka gabatar mata, cikin takardar da B20 ya fitar, bai nuna ra'ayoyinsu yadda ya kamata ba, lamarin da ya lahanta ka'idar yin shawarwari domin cimma matsaya guda ta taron B20. (Maryam)