Shugabannin kungiyar G20 sun lashi takobin inganta hadin kai don yaki da ayyukan ta'addanci da masu samar musu da kudi, a jiya Jumma'a, rana ta farko na taron da suke a birnin Hamburg na Jamus.
Wata sanarwar da aka fitar a jiyan ta ce, shugabannin kungiyar kasashe masu karfin masana'antu da tattalin arziki a duniya, wadanda ke samar da kashi 85 cikin dari na kayyayaki a duniya, sun jadadda cewa, akwai bukatar aiwatar da dukkan matakan yaki da ta'addanci bisa biyayya da ka'idojin MDD da dukkan dokokin kasa da kasa.
Shugabannin sun amince su gaggauta musayar bayanai tare da amfani da duk hanyoyin dake akwai na musayar bayanai, musammam ma hanyoyi musayar bayanai na rundunar 'yan sanda ta kasa da kasa wato INTERPOL.
Game da hanyoyin da 'yan ta'adda ke samun kudi kuwa, shugabannin sun tabbatar da kudurinsu na katse dukkan hanyoyi da dabarun samar da kudaden, suna masu kira da a gaggauta aiwatar da kudurin kwamitin sulhu na MDD da na hukumar yaki da cin hanci da datse hanyoyin samun kudi ga 'yan ta'adda yadda ya kamata a fadin duniya, domin karfafa matakan yaki da hanyoyin samun kudi na kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya. (Fa'iza Mustapha)