Shugabannin kungiyar G20 sun cimma ra'ayi daya kan inganta dunkulewar kasa da kasa, inda suka yi alkawarin bude kasuwanninsu, da kuma nuna kin amincewa saka shinge a fannin ciniki. Haka kuma, sun tsaida kudurin kafa wani tsarin ciniki na kasa da kasa domin ciyar da harkokin zuba jari a tsakanin kasa da kasa gaba.
Amma, shugabannin kungiyar ba su cimma ra'ayi daya kan batun yarjejeniyar Paris ba, sabo da janye jikin da kasar Amurka ta yi daga wannan yarjejeniya.
Amma, abin farin cikin shi ne, sauran mambobi guda 19 da yarjejeniyar ta shafa sun nuna cewa, za su ci gaba da goyon bayan wannan yarjejeniya, in ji shugaba Merkel.
Bugu da kari, an zartas da rahoton taron shugabannin kungiyar G20 na birnin Humburg, inda aka yi alkawarin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa sakamakon da aka cimma a lokacin taron kungiyar da aka yi a birnin Hangzhou na kasar Sin, domin inganta harkokin zuba jari da dauwamammen ci gaban kasashen duniya, da kuma kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu da kasashen Afirka, ta yadda za a nemi daidaituwa da kuma dauwamammen ci gaban kasa da kasa, domin tallafawa al'ummomin duniya baki daya. (Maryam)